Connect with us

Featured

Mutane Biyu Ne Su Ka Mutu a Ginin Da Ya Faɗo Kan Mutane a Lagos – NEMA

Hatsarin ya auku a unguwar Oyingbo da ke Jihar Legas, inda wani ginin bene mai hawa biyu ya rushe a daren Litinin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, yayin da aka ceto mutane 20 da ransu. Hukumar Kula da Bala’o’i ta Kasa (NEMA) ce ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami’anta sun jagoranci aikin ceto tare da hadin gwiwar LASEMA da sauran hukumomin agaji.

 

A cewar NEMA, mutanen da suka tsira an kai su asibitoci domin jinya, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane biyu. Hukumar ta ce an kammala aikin bincike da ceto, inda jami’an ‘yan sanda suka ci gaba da tsare wurin don kauce wa taruwar jama’a.

 

Rahotanni sun nuna cewa ginin da ya rushe ya dade da samun matsaloli, kuma Hukumar Kula da Gine-gine ta Jihar Legas (LASBCA) ta taba yin gargaɗin rushe shi saboda hatsarin da ke tattare da shi, amma masu zama a ciki su ka ki barin wurin. Wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa alamun karyewar ginin sun bayyana tun kafin hadarin.

 

Wata mazauniya mai suna Mrs Adaeze ta ce ta yi asarar kaya masu daraja bayan ginin ya rushe, tana rokon gwamnati ta tallafa musu. Haka kuma wani mazaunin yankin, Habeeb Jamiu, ya bayyana cewa hatsarin ya faru bayan ruwan sama mai karfi, inda suka ji kukan mutanen da suka makale a cikin gine-ginen kafin masu agaji su isa. Hukumar NEMA ta sake jaddada bukatar jama’a su rika bin umarnin jami’an tsaro da na lafiya domin guje wa irin wannan asara mai ciwo.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet