Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Sun Ceto ƴan Kasashen Waje 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Rundunar ‘Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya Abuja ta samu nasarar kubutar da mutum 23 ‘yan kasashen waje da aka yi garkuwa da su a Nasarawa, tare da cafke mutum 14 daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 8 na dare ranar Talata, 22 ga Oktoba, a unguwar Angwan Adamu Ruga Fulani Zone B, yankin Ado Mararaba, bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri.

Binciken farko ya nuna cewa wani shahararren ɗan ta’addar ƙetare mai suna Abubakar Jigiba, wanda ke da mafaka a ƙasashen Côte d’Ivoire, Ghana, Mali da Najeriya, shi ne ke jagorantar wannan ƙungiya. Ana zargin ƙungiyar da jawo waɗannan mutanen zuwa Najeriya da alƙawarin samar musu da aiki mai albashi, sai dai daga bisani suka tsare su suna neman kuɗin fansa har CFA miliyan 4 (Naira miliyan 10) daga kowannensu ta hanyar WhatsApp da sauran kafafe.

An ce an rufe waɗanda aka sace a cikin gidaje biyu, inda aka tsare su cikin mawuyacin hali. Daga cikin waɗanda aka kubutar akwai maza 14, mata takwas, da ƙaramin yaro ɗaya. Babu wanda ya rasa ransa, sai mutum ɗaya da ya samu rauni a kunne, wanda aka garzaya da shi Asibitin Ƙasa, Abuja, don jinya.

Rundunar ‘yan sanda ta ce bincike na ci gaba da neman shugaban ƙungiyar da ɗan uwansa, Sougule Zoubere, waɗanda suka tsere. Kwamishinan ‘yan sanda na FCT, CP Miller Dantawaye, ya yaba wa Scorpion Squad bisa wannan nasara, tare da kiran jama’a su rika bayar da rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargin ba na halal ba a yankunansu, musamman a kan iyakokin Abuja da Nasarawa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet