Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Iƙirarin Trump Na Kisan Kiristoci a Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karyata ikirarin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa ana kashe Kiristoci da yawa a kasar, wanda ya sa ya sanya Najeriya cikin jerin “kasashen da ake kallon suna tauye ’yancin addini.” A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, gwamnati ta bayyana cewa wannan zargi bai nuna ainihin halin da ake ciki a kasa ba, inda ta ce ’yan Najeriya na rayuwa tare cikin lumana ba tare da wariyar addini ba.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana ci gaba da yaki da ta’addanci tare da karfafa zumunci tsakanin mabambantan addinai, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da hulɗa da Amurka ta hanyar diflomasiyya domin fahimtar juna da inganta hadin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

A wani sako da Trump ya wallafa a Truth Social, ya ce Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya, inda ya zargi “’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi” da kisan mutane dubban-dubban. Ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta duba lamarin da gaggawa, yana mai cewa “Amurka ba za ta yi shiru yayin da ake kashe Kiristoci a Najeriya ba.”

Sai dai Ministan Bayani da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana a CNN cewa ’yan ta’adda a Najeriya ba su keɓe addini guda daya ba wajen kai hari. Ya ce “musulmai da kiristoci duka na fuskantar hare-hare,” musamman a yankin Arewa. Haka zalika, Majalisar Tarayyar Turai ta bukaci Najeriya da ta karfafa kariya ga al’ummomin da ke cikin hadari da kuma tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet