Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Umarci Shugabannin Ƙananan Hukumomi Su Tashi Tsaye Don Magance Matsalar Tsaro

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarni ga dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar su riƙa gudanar da tarukan tsaro a kai a kai, domin ƙarfafa tattara bayanan sirri da wayar da kan al’umma kan batun tsaro. Wannan mataki na zuwa ne bayan wani taron kwamitin tsaro da aka gudanar a fadar gwamnati, inda aka tattauna yadda za a inganta hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Wannan umarni ya biyo bayan harin ‘yan bindiga da aka kai a kauyen Faruruwa na karamar hukumar Shanono, inda aka kashe mutum ɗaya, aka sace dabbobi da kuma fasa shagunan waya. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun isa kauyen ne a kan babura fiye da 25, abin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

A yayin taron, an jaddada muhimmancin gudanar da irin waɗannan tarukan tsaro a matakin ƙananan hukumomi domin gano barazanar tsaro tun da wuri, da kuma tabbatar da saurin daukar mataki kafin ta ta’azzara. Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wasu yankuna kamar Shanono, Tsanyawa, Tudun Wada, Doguwa da Gwarzo na bukatar kulawa ta musamman saboda yawan barazanar da suke fuskanta.

Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga wadanda harin ya rutsa da su tare da tabbatar wa da jama’ar Kano cewa gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan da ke kusa da iyakokin jihar da ke fuskantar barazanar ‘yan bindiga.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet