Featured
Na Kusa Daina Buga Ƙwallon Ƙafa – Cristiano Ronaldo
Shahararren ɗan wasan ƙwallon kafa na Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa ya kusa yin bankwana da buga kwallo bayan tsawon shekaru yana haskakawa a fagen wasanni. A wata hira da ya yi da Piers Morgan, Ronaldo wanda yanzu yake taka leda a Al Nassr dake Saudiyya, ya ce lamarin zai kasance mai cike da ƙunci da hawaye, amma ya shirya don fuskantar sabon babi na rayuwa. Ronaldo ya kusan cimma tarihin zura kwallaye 1000, inda a yanzu ya zura kwallaye 952, abin da ya sanya shi ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasa a tarihin ƙwallon duniya.
Ronaldo ya ce tun yana saurayi yake shirin rayuwarsa bayan kwallon kafa, don haka ba zai daina shiri ba. Ya bayyana cewa zai fi mayar da hankali kan iyalinsa da jin daɗin rayuwa, sannan kuma zai kasance kusa da yaransa musamman don sanya su kan madaidaiciyar hanya. Ya ambaci cewa ɗansa Cristiano Junior da ɗan’uwansa Mateo suna da sha’awar ƙwallo, sannan yana son kallon yadda rayuwar su za ta ci gaba.
Tsohon tauraron Manchester United da Real Madrid ya bayyana cewa duk da zurfin soyayyarsa ga kwallo, babu wani abu da zai maye gurbin jin daɗin zura kwallo a raga. Sai dai ya jaddada cewa duk abu yana da farkonsa da ƙarshe, kuma lokaci ya yi da zai ba kansa hutu da yin abubuwan nishadi. Daga ciki ya ambaci wasan Padel wanda yake bugawa tare da abokansa.
Ya kuma yi tsokaci game da tsohuwar kungiyarsa Manchester United, yana mai cewa ba za a iya tsammanin mu’ujiza daga sabon koci Ruben Amorim ba. A cewarsa, kungiyarsu tana bukatar canje-canje daga cikin gida domin dawowa kan hanya. Duk da haka, Ronaldo ya tabbatar da cewa Manchester United har yanzu tana cikin zuciyarsa kuma yana son ganin ta koma matsayin da duniya ta santa.
