Connect with us

Featured

Har Yanzu Gwamnatin Tarayya Bata Bamu Abinda Ta Yi Mana Alƙawari Ba – ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa har yanzu ba ta ga kudi N50bn na farfado da jami’o’i da gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa ta saki ba. A wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labaran ASUU, Farfesa Jurbe Molwus, ya fitar a ranar Laraba, kungiyar ta ce ko daya daga cikin bukatun da ta gabatar ba a cika shi ba, duk da cewa ta dakatar da yajin aikin gargadi na mako biyu bisa amincewar gwamnati za ta magance matsalolin.

ASUU ta ce kafin taron Majalisar Koli ta kasa da za ta gudanar a ranar 8 da 9 ga Nuwamba, 2025, ta zata gwamnati ta riga ta biya wasu hakkoki kamar albashin watanni 3.5 da aka riƙe, ragowar kudaden karin albashi na 25/35%, bashin karin girma, da kuma albashin wasu mambobi da aka dakatar. Amma sai dai ta ce abin da ta gani kawai shi ne sanarwar gwamnati a kafafen yaɗa labarai ba tare da an ga bayanai a asusu ba.

Kungiyar ta kuma kalubalanci Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, bayan da ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta biya N2.3bn don rufe bashin albashi da karin girma a jami’o’i. ASUU ta ce adadin kudin da aka ambata ba zai biya bukatun ma’aikatan jami’o’i ba, ballantana a ce zai wadata jami’o’i da dama a fadin kasar. Ta ce wannan adadi ba komai ba.

ASUU ta gargadi cewa za ta koma yajin aiki idan gwamnati ta gaza biyan bukatunta kafin ranar 21 ga Nuwamba, 2025, wato karshen wa’adin mako hudu da ta bai wa gwamnati. Kungiyar ta bukaci dalibai, iyaye da al’umma su matsa lamba ga gwamnati domin kaucewa komawa barace-barace a jami’o’i.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet