Connect with us

Featured

Sojoji Sun Tseratar Da Ƴan NYSC Daga Faɗawa Hannun Boko Haram a Borno

Dakarun haɗin gwiwa na Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas sun ceci matasa 74 masu aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) da suka makale a hanyar Buratai–Kamuya da ke jihar Borno, bayan motocinsu sun lalace a kusa da sansanin da ake zargin ‘yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP ke kai hare-hare.

Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba, ya bayyana cewa an ceto matasan — maza 36 da mata 38 — da misalin ƙarfe 9 na dare ranar Talata, bayan na’urorin CCTV da ke sa ido suka gano motsin motocin su uku a yankin da aka fi sani da hadari. Sojoji suka isa wurin da gaggawa, inda suka tarar da su cikin halin damuwa kuma suka taimaka musu kafin ‘yan ta’addan su kai hari.

Uba ya ƙara da cewa, matasan suna cikin kulawar sojoji a sansanin Buratai domin tsaro kafin a kaisu zuwa wuri mafi aminci. Wannan aikin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan sojojin suka kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu 29 da ake zargin masu taimaka wa ‘yan ta’adda ne a jihar Borno.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet