Connect with us

Featured

Tinubu Ya Ɗage Tafiyarsa Zuwa Afrika Ta Kudu Sakamakon Hare-haren Da Suka Faru a Kebbi Da Kwara

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya jinkirta tafiyarsa zuwa taron shugabannin G20 a ƙasar Afirka ta Kudu, saboda samun sabbin rahotannin tsaro game da sace ɗalibai mata a Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, jihar Kwara. Tinubu ya ce yana jiran cikakken bayanin mataimakinsa, Kashim Shettima, da hukumomin tsaro kafin ya yanke sabon mataki.

A wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan labaru, Bayo Onanuga, an bayyana cewa shugaba Tinubu ya ba da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Eruku da yankunan da abin ya shafa a Kwara, bayan da Gwamnan jihar ya nemi taimako. Hakanan shugaban ƙasar ya ce dole ne a bi sawu a cafke ’yan bindigar da suka kai harin.

A Kebbi kuwa, Tinubu ya nuna takaici kan sace dalibai 25 na makarantar sakandaren ’yan mata ta Maga, inda ’yan bindiga suka hallaka mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin kare dalibansa. Shugaban ya tabbatar wa iyayen yaran da gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don ceto su ba tare da lahani ba, tare da jajanta wa sojojin da suka yi rashi a Borno, ciki har da Brigadier Janar Musa Uba.

Tinubu, wanda ya riga ya samu hasashen rahotannin soja kan yiwuwar harin kafin faruwar sa, ya tura Mataimakinsa Shettima zuwa Kebbi domin ganawa da shugabannin yankin da kuma duba halin da ake ciki. Ya ce batutuwan tsaron ƙasa sun fi muhimmanci a yanzu, don haka ya dage dukkan shirinsa na tafiya zuwa Afirka ta Kudu da Angola har sai an kammala bincike da bayar da rahotanni na gaggawa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinovdcasinoholiganbetmarsbahissahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet