Connect with us

Featured

Tinubu Ya Umurci Ministan Tsaro Ya Koma Kebbi Da Zama Har Sai An Ceto Ɗaliban Da Aka Sace

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi nan da nan domin jagorantar ayyukan ceton ɗaliban mata da aka sace daga makarantar sakandare ta ‘Government Girls Comprehensive Secondary School’, Maga, a farkon makon nan. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Matawalle zai zauna a jihar domin sa ido a kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka. An sace akalla ɗalibai 24 ne bayan wasu ‘yan bindiga sun kutsa makarantar da misalin ƙarfe 4:00 na asuba a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Kebbi ta ce maharan sun zo dauke da makamai, suna harbi sama domin tsoratarwa kafin su tafi da yaran cikin daji. Haka kuma, wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Matawalle zai jagoranci haɗin gwiwar sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da aka tura wajen farautar masu garkuwar. Ana ganin kwarewarsa a lokacin da yake Gwamnan Zamfara (2019–2023), lokacin da lamarin sace-sacen ɗalibai ya yi kamari, na da amfani a wannan aiki.

A wani bangare kuma, gwamnonin jam’iyyar APC ƙarƙashin Progressive Governors’ Forum (PGF) sun kai ziyarar jaje ga Gwamna Nasir Idris na Kebbi, inda suka bayyana lamarin a matsayin mummunar barna da ta sanya damuwa a zukatan jama’a. Kakakin kungiyar, Gwamna Hope Uzodinma, ya ce za su ci gaba da mara wa gwamnati baya domin ganin an magance matsalar tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet