Connect with us

Featured

Boko Haram Sun Sace Mata 12 a Borno

A kalla mata 12 ne aka sace a yankin Mussa na ƙaramar hukumar Askira-Uba, jihar Borno, bayan wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun tare su da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonaki. Wannan mummunan hari ya tayar da hankula a yankin tare da kira ga gaggawar matakan tsaro daga hukumomi da shugabanni na al’umma.

A wani hari dabam da ya faru daren Lahadi, mayakan Boko Haram sun kai farmaki a ƙaramar hukumar Magumeri da misalin ƙarfe 1:15 na safe, inda suka ƙone gidaje, shaguna da motocin jama’a a tsawon sama da sa’o’i biyu. Sai dai rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ba a rasa rai ba, bayan hadin guiwar jami’an tsaro da CJTF da suka yi nasarar korar maharan wajen ƙarfe 3 na safe.

Rahotannin da Kakaki24 ta tattara sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar ta ce an fara bincike kan sace matan tare da ƙara tabbatar da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa. Mazauna yankin sun bayyana fargaba tare da neman daukar mataki cikin gaggawa domin kare rayukan manoma musamman a lokacin dawowa daga gonaki.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ayyana ranar Litinin, 24 ga Nuwamba, a matsayin ranar azumi da addu’a a fadin jiharsa domin neman taimakon Ubangiji kan matsalar tsaro da rikice-rikicen da ke addabar al’umma. Ya yabawa jajircewar jama’a da goyon bayansu ga dakarun tsaro, yana mai cewa addu’a da hadin kai sun taka muhimmiyar rawa a kokarin maido da zaman lafiya.

Tare da haka, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi kira ga shugabannin Arewa su tashi tsaye tare da hada kai domin magance kalubalen tsaro da suka yi kamari a yankin. Ya ce Arewa na da karfin da ake bukata domin shawo kan lamarin muddin akwai hadin kai da tsari mai kyau daga hukumomi da shugabanni.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet