Connect with us

Featured

Kwastam Ta Kama Dala Miliyan $2.2 a Filayen Jiragen Saman Najeriya Cikin Watanni 7

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta gano kuma ta kama dala miliyan $2.2 a manyan filayen jiragen sama na ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Yuli 2025. Babban Kwanturola na NCS, Bashir Adewale Adeniyi, shi ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki kan inganta ayyukan jiragen sama da aka gudanar a Abuja. Daga cikin kudaden da aka kama, akwai $193,000 da aka boye cikin akwatunan yoghurt a Abuja ranar 20 ga Maris, $1,154,900 da SR135,900 da aka kama a Kano daga wani matafiyi daga Saudiyya, sai kuma $578,000 da aka kama a Lagos daga wani da ya bayyana bayanai na ƙarya.

A cewar NCS, kamun kudaden ya zama nasara ne sakamakon tsaurara dokar bayyana kudade da kuma bin ka’idar takardun izinin shigo da kaya, wanda ya karfafa tsaron iyakokin kasar. Haka kuma hukumar ta kama kudaden kasashen waje da darajarsu ta kai N653.99 million a Kano, tare da kama haramtattun kayayyaki irin su makamai, da miyagun kwayoyi bisa hadin kai tsakanin NCS da FAAN, NDLEA, da NCAA. Hukumar ta ce waɗannan matakan sun taka rawa wajen karya hanyar masu safarar kudade da kayayyakin da ake boyewa da kuma hana miyagun laifuka yaduwa.

Rahoton KAKAKI24 ya tabbatar da cewa hukumar ta kuma bankado kayan fatauci da kudinsu ya haura N1.2 biliyan, ciki har da shinkafa ta waje, motocin da aka riga aka yi amfani da su da magungunan da ba su da rajista. Har ila yau, NCS ta bayyana cewa ta samar da kudaden shiga har N3.7 tiriliyan a rabin farkon shekarar, inda hukumar filin jirgin sama na Lagos ta bayar da N97.16 biliyan, wanda ya karu da kaso 20.92 cikin 100 daga shekarar da ta gabata. Hukumar ta ce sabbin injinan duba kaya na zamani kamar Orion 928DX sun rage duba kaya da hannu, tare da inganta jin dadin fasinjoji, yayin da tsarin AEO ya rage lokacin tantance kaya daga awanni 168 zuwa 43.

NCS ta kara da cewa a matakin gaba za ta fadada hadin kai da hukumomin jiragen sama domin saukaka bincike, karfafa tsaro da kuma bunkasa cinikayya. Hukumar ta ce ci gaba da inganta fasaha, horar da jami’ai da kula da iyakoki na da rawar gani wajen rage kutsen kudade da kayayyakin da ake boyewa a filayen jiragen sama. Ta jaddada cewa duk wani kama kayayyaki ko kudade shaida ce ta jajircewa da hadin kai wajen kare martabar kasa da sirrin zirga-zirgar tashoshin jiragen sama.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet