Connect with us

Featured

ECOWAS da AU Sun Yi Allah-wadai Da Juyin Mulki a Guinea-Bissau

Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ECOWAS da West African Elders Forum sun soki dakatar da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da na ’yan majalisa a Guinea-Bissau da kuma karɓar mulki da sojoji suka yi. A wata sanarwa da shugabannin tawagar sa-ido na zabe suka fitar, sun bayyana abin da ya faru a matsayin yunkurin katse tsarin dimokuradiyya. Sun tabbatar da cewa sun gana da manyan ’yan takara biyu – Shugaba Umaro Embalo da abokin hamayyarsa Fernando Dias – wadanda suka yi alkawarin karɓar sakamakon zabe cikin natsuwa kafin sojoji su sanar da kwace iko.

Sanarwar ta kuma yi tir da yadda sojoji suka dakatar da shirin sanar da sakamakon zabe, suka rufe iyakokin kasar tare da mamaye hanyoyin da ke kaiwa fadar shugaban kasa bayan harbe-harben da aka ji a yankin. Janar Denis N’Canha, ya karanta sanarwar daukar mulki tare da zargin gano wani makirci na ’yan safarar miyagun kwayoyi da ake cewa sun shigo da makamai domin rikita tsarin mulki. Haka kuma hukumomin soja sun dakatar da shirye-shiryen gidajen yada labarai tare da kakaba dokar hana fita.

A bayanan da KAKAKI24 ta tattara, kungiyoyin sa-ido sun bukaci a dawo da tsarin mulki cikin gaggawa tare da sakin jami’an zabe da aka tsare domin kammala aikin sanar da sakamakon. Sun kuma bukaci al’ummar kasar da su zauna lafiya, suna mai jaddada muhimmancin zaman lafiya, kwanciyar hankali da kare mutuncin jama’ar Guinea-Bissau a wannan lokaci. Kungiyoyin sun bayyana cewa abin takaici ne ganin sanarwar juyin mulki ta zo jim kadan bayan samun tabbacin karɓar sakamakon zabe daga ’yan takara.

Guinea-Bissau dai ta yi kaurin suna wajen rikice-rikicen siyasa, inda ta fuskanci juyin mulki hudu tun bayan samun ’yancin kai, tare da yunkurin juyin mulki da dama. Wannan sabon daukar mulki ya sake tayar da damuwa a yankin Yammacin Afrika, inda kasashe ke fama da barazanar dusashewar dimokuradiyya da yawaitar tsoma bakin sojoji cikin siyasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet