Connect with us

Featured

An Gano Sunayen Ƴan Boko Haram a Jerin Masu Neman Aikin Soja a Najeriya

Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Idris Wase, ya bayyana cewa an taba gano sunayen wasu da ake zargi da Boko Haram da sauran ’yan ta’adda a cikin jerin sunayen masu neman aikin soja da ’yan sanda a Najeriya. Ya fadi hakan ne yayin wani zaman musamman da Majalisar ta gudanar kan halin tsaro da ya tsananta a fadin kasar, inda ya gargadi cewa shigar da miyagun mutane cikin hukumomin tsaro na iya jefa kasa cikin hadari mai girma. Wase ya ce zai iya tabbatar da batun tare da tsohon shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisa, Mukhtar Betara, yana mai jaddada cewa akwai lokutan da aka samu sunayen barayi da masu laifi a cikin wadanda aka tantance domin aikin tsaro.

Wase ya kara jan hankalin ’yan majalisa cewa kin tsayawa kan ka’ida wajen ba da takardun neman aiki ga masu kwadayin shiga rundunonin tsaro na taimakawa wajen lalata tsaron kasa. Ya bayyana cewa ya rasa dan uwa, dan ammi da dan yayansa sakamakon hare-haren ’yan ta’adda, tare da bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya na dauke da kaso 52% na matsalolin tsaro a kasar. Ya kuma bayyana yadda wani karamin dan uwansa ya roki a dauke shi daga yankin da rikice-rikice suka yi katutu saboda tsoron rasa rayuwa. Haka kuma ya bukaci sake duba umarnin fadar shugaban kasa na janye ’yan sanda daga aikin gadin manyan jami’ai saboda hadarin da hakan ka iya jawowa idan ba a fayyace tsari ba.

A yayin tattaunawar, KAKAKI24 ta bibiyi martanin sauran wakilai daga sassa daban-daban na kasar, inda wakilin Arewa maso Yamma, Sada Soli, ya bayyana cewa matsalar tsaron yankinsu na da sarkakiya, wadda ta samo asali daga laifuka, matsalolin muhalli, karancin gwamnati da matsin tattalin arziki. Ya jaddada cewa daukar matakin bindiga kawai ba zai magance lamarin ba, yana mai cewa bukatar da ake da ita ita ce hade tsare-tsaren tsaro da gyare-gyare a harkar noma, kiwo, mulki da farfado da tattalin arzikin al’umma. A nasa bangaren kuma, Betara ya bayyana Arewa maso Gabas a matsayin “tushen ta’addanci da rikice-rikicen kabilanci”, inda ya tunasar da mummunan kisan Baga na 2015 da hare-haren bam da suka hallaka fararen hula da jami’an tsaro.

Wani Sanata daga Kudu maso Kudu, Solomon Bob, ya zargi gwamnatoci tun daga 1999 da gazawa wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa suna sulhu da ’yan ta’adda maimakon daukar matakin doka. Shugabar Kwamitin Harkokin Mata ta Majalisa, Kafilat Ogbara, ta nuna takaici kan yadda matsalar tsaro ke addabar mata da yara musamman bayan sace-sacen da suka faru a Papiri da Kamba, tana mai cewa wannan na nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet