Connect with us

Featured

AHIP Ta Horar Da Ƙungiyoyin Farar Hula Da Na Mata Kan Dokokin ECOWAS Da Haƙƙoƙin Ƴan Ci-rani

Ƙungiyar Adolescent Health and Information Project (AHIP), ƙarƙashin shirin ROOTS (Resilient Opportunities for Outreach, Trade and Sustainability), tare da haɗin gwiwar International Organization for Migration da tallafin European Union, ta gudanar da horon kwanaki uku ga ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin mata kan dokokin ECOWAS da haƙƙin baƙi. An gudanar da horon daga ranar 9 zuwa 11 ga Yuni, 2026 a Gidan AHIP da ke Maiduguri Road Kano, inda mahalarta suka samu ilimi kan ‘yancin zirga-zirga, zama da gudanar da kasuwanci a ƙasashen ECOWAS.

Shugabar AHIP, Hajiya Mairo Bello, ta bayyana cewa an shirya horon ne domin wayar da kan jama’a game da muhimmancin mallakar ingantattun takardun tafiye-tafiye. Ta ce mutane da dama, musamman mata da matasa, na shiga ƙasashen waje ba tare da cikakkun takardu ba, lamarin da ke jefa su cikin matsaloli kamar cin zarafi, fataucin bil Adama, da kuma rashin samun damar amfani da wasu muhimman ayyuka kamar buɗe asusun banki.

A yayin horon, an tattauna batutuwa da suka haɗa da hanyoyin hijira masu inganci da marasa inganci, haƙƙin baƙi, kariyar mata da yara, tasirin sauyin yanayi ga hijira, da rawar da ƙungiyoyin farar hula ke takawa wajen kare masu hijira. Mahalartan sun kuma yi tattaunawar rukuni–ruuuni tare da gabatar da tsare-tsaren da za su aiwatar a al’ummominsu.

A ƙarshe an bai wa mahalarta taron takardar shaidar horon, yayin da Kakaki24 ta zamo daya daga cikin wakilan yan jarida a taron.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet