Featured
Shugaban Saliyo Ya Maye Gurbin Tinubu A Matsayin Sabon Shugaban ECOWAS
Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja.
Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa.
Tinubu ya ce wajibi ne ƙasashen yankin su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.
Yayin da yace yana da kyau su ƙara inganta haɗin kai, mutunta ƙa’idojin diflomasiyya, da tabbatar da ci gaba wanda zai haɗa kowa da kowa musamman matasa, mata da waɗanda ke cikin mawuyacin hali,” in ji Tinubu.
A jawabinsa na karɓar shugabanci, Shugaba Bio ya gode wa Tinubu bisa jagoranci mai cike da hangen nesa da kyakkyawan fata.
Inda yace a lokacin Shugabancin tinubu a ECOWAS ya nuna jajircewa wajen ƙarfafa tattaunawar yankin, farfaɗo da tattalin arziƙi da wanzar da zaman lafiya.
Yayin da yace Shi ma zai yi kokarin ɗaukar wannan nauyi domin ci gaba daga inda shugaba Tunibu ya tsaya.
Shugaba Bio ya bayyana cewa akwai buƙatar ECOWAS ta ƙara dagewa wajen kare dimokuraɗiyya, inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi.
Ya kuma ce dole a sake fasalin ECOWAS ta yadda za ta zama mai gaskiya, inganci da amsa buƙatun al’ummarta.
Ya kuma bayyana matsalolin da yankin ke fuskanta kamar ta’addanci, taɓarɓarewar siyasa da matsin tattalin arziki.
Yayin da yace a Fagen dimokuraɗiyya ana fuskantar ƙalubale a sassa daban-daban inda a wasu ƙasashe tuni tsarin mulki ya rikiɗe.
A karshe ya bayyana cewa , zai yi jagoranci ECOWAS cikin gaskiya da fifita buƙatun al’umma tare da inganta haɗin kan yankin.
