Featured
An Kama Ƴan Najeriya 50 a India Kan Laifin Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi
A ranar Alhamis 28 ga Nuwamba 2025, rahotanni daga India sun tabbatar da cafke ’yan Najeriya 50 a wani babban samamen da ’yan sanda suka kai kan wata babbar kungiyar safarar miyagun kwayoyi. Rahoton NDTV ya ce an yi samamen ne a birnin Delhi tare da hadin gwiwar rundunar EAGLE ta Telangana. Hakan ya biyo bayan watanni na tattara bayanan sirri. An ce kungiyar tana yada meth da cocaine a fadin kasar.
Hukumar ta gano cewa kungiyar na amfani da hanyoyi irin na manhajojin isar da kaya, domin kauce wa ganawa da mutane kai tsaye. Hakanan suna amfani da sakonni da aka kulle don boye bayanai. Rahoton ya ce an gano kusan mutane 2,000 da aka rika isar wa da kwayoyi ta hanyar “dead drop.” Hakan na nuna illar irin yadda kungiyar ke sarrafa kasuwa. Rahotanni sun ce ma da fannin karuwanci suke boye harkarsu.
Kakaki24 ta tattara bayanai cewa hukumar ta kuma gano cewa kudaden da ake samu daga safarar kwayoyin ana bi da su ta hanyar hawala, inda ake juya su zuwa kaya kamar gashin mutum da kayan sakawa, sannan a tura su Lagos a matsayin halal. Wani daga cikin jagororin kungiyar ana zargin ya wanke kudin har zuwa ₹15 crore.
Rahotannin PUNCH Metro sun ce an dade ana kama ’yan Najeriya a birane daban-daban kan safarar kwayoyi. Amma wannan samame da aka kama mutum 50 shi ne mafi girma a baya-bayan nan. Hukumomin India sun ce mataki na gaba shi ne ci gaba da bincike kan masu aikin hawala da shugabanin kungiyar da ke kasashen waje. Sun ce wannan babbar nasara ce wajen dakile wannan gagarumar cibiyar miyagun kwayoyi.
