Connect with us

Featured

Rundunar Ƴansanda Ta Sha Alwashin Baiwa Mata Manyan Muƙamai a Hukumar

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sha alwashin ƙara bai wa mata manyan mukamai a sashen dabaru, aiki, da kuma shugabanci. Ya bayyana haka a bikin cika shekaru 70 da fara aikin mata a rundunar ‘yan sanda da aka gudanar a Abuja.

Egbetokun ya ce rundunar na alfahari da matan ‘yan sanda, yana kuma ba da tabbacin dakile wariya, cin zarafi ko toshe wa mata hanya wajen haɓaka ƙwarewa. Ya jaddada cewa matan da ke shigowa yanzu ba kawai suna gado ba ne, suna kuma gina sabon babi na aikin tsaro mai cike da ƙwarewa, tausayi da jarunta.

A tattaunawarsa, ya bayyana cewa ana bibiyar wannan ci gaban da ya faro tun 1955, duk da cewar a baya mata sun taɓa takaita ga ayyukan yara, rubutu da al’amuran mata. Ya ce duk da matsalolin da aka taɓa fuskanta, matan ‘yan sanda sun kafa sabon mizani na ƙwarewa da mutunta aiki.

IGP Egbetokun ya ƙara da cewa mata yanzu sun samu matsayi a dukkan matakai – daga dabaru zuwa bincike, gudanarwa da manyan mukamai. Ya ce wannan tafiya tana nuni da ƙarfin hali, katuwar jajircewa da sadaukarwar mata wajen kare ƙasa da samar da tsaro mai dorewa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet