Connect with us

Featured

Daƙile Juyin Mulki a Benin Ya Nuna Ƙarfin Tasirin Tinubu a Yammacin Afirka – Fadar Shugaban Ƙasa

A wani jawabi da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa martanin da Najeriya ta yi game da yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya nuna irin ƙarfin jagoranci da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ke da shi wajen kare zaman lafiya da tsarin mulki a yankin Yammacin Afirka. Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2025, lokacin da wasu sojoji ƙarƙashin “Kwamitin Sake Ginin Soja” suka mamaye gidan talabijin na ƙasar tare da ayyana hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun gwamnati sun fatattaki waɗanda suka yi yunkurin karɓe mulki cikin gaggawa, lamarin da ya sa gwamnatin Benin ta shaida cewa an dakile wannan yunƙuri ba tare da ɓata lokaci ba. A wata sanarwa da mataimakin Shugaban Najeriya kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ya wallafa a dandalin X ranar Litinin, ya ce matakin da Najeriya ta ɗauka na hanzari ya nuna cikakken jajircewar Tinubu wajen kare tsarin mulki a sub-region.

A cikin rahotonsa, Kakaki24 ta rawaito cewa sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa ta ce martanin gaggawa da Najeriya ta bayar—musamman ta fuskar Allah wadai da yunkurin—ya taimaka wajen tsara amsar da ƙasashen yankin suka bayar, tare da ƙarfafa matsayar rashin yarda da duk wani yunƙurin karɓe mulki ta hanyar doka-ta-ɓaka. Sanarwar ta ƙara da cewa matsayin Tinubu ya yi daidai da na ECOWAS, musamman ganin cewa a matsayinsa na shugaban ƙungiyar, ya dade yana jan hankali cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen juyin mulki a yankin.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan yunkuri da bai yi nasara ba ya sake tunasar da kasashen yankin raunin da ke tattare da sauyin mulki, amma kuma ya tabbatar da muhimmancin jagoranci nagari. Ta ce dalilin da yasa Najeriya ta tsaya kan matsayin demokradiyya shi ne kare makomar Benin musamman yayin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaben 2026. A cewar gwamnatin Najeriya, jajircewar Tinubu wajen tsayawa kan doka da oda ita ce ginshikin da ke bai wa Yammacin Afirka kwarin gwiwar gaba mai ɗorewa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet