Connect with us

Featured

Kwankwaso Ya Jinjinawa Abba Kabir Yusuf Kan Kyakkyawan Shugabancin Da Yake Gudanarwa a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa abin da ya kira gagarumin ci gaba da gwamnatin Kano ke samu a karkashin shugabancinsa. Ya bayyana hakan ne lokacin da Gwamna Yusuf ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke Abuja domin miƙa masa lambar girmamawar da aka ba shi a wani biki na ƙasa.

Kwankwaso, wanda ya yi mulkin Kano sau biyu, ya ce kyautar da aka ba Gwamna Yusuf ta fito ne daga “ingantattun ayyukan gine-gine da cigaban zamantakewa” da ake gani cikin kankanin lokaci. Ya ce wannan nasara tana nuna cewa jihar Kano ta koma tafarkin mulki mai ma’ana da fifita bukatun al’umma.

A yayin ziyarar, Gwamna Yusuf ya mika masa lambar “Distinguished Award for Visionary Leadership and Public Service Sector Reform” wacce ya karɓa a Abuja. Kwankwaso ya yi addu’a tare da tabbatar wa gwamnan cikakken goyon bayan sa.

Kwankwaso ya bukaci Gwamna Yusuf da ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da tsare-tsare na inganta walwalar jama’a, yana mai bayyana cewa mutanen Kano na ganin canji kai tsaye sakamakon ayyukan da ake gudanarwa a faɗin jihar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet