Connect with us

Featured

Gayyatar Da EFCC Ta Yi Min Bashida Alaƙa Da Ta’addanci – Malami

Tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa tambayoyin da Hukumar EFCC ta yi masa ba su da alaƙa da ta’addanci, safarar kuɗi ko mallakar asusun banki da dama, illa dai bayanin zargin sake dawowar kudaden Abacha ne kawai. Malami ya ce labaran da ake yadawa cewa jami’an tsaro ko hukumomi a ƙasashen waje sun zarge shi da ta’addanci “karya ne marar tushe.”

A cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce EFCC ta gayyace shi ne don fayyace batun zargin maimaita dawo da dala miliyan $310 na kudaden Abacha a lokacin gwamnatin Buhari. Ya ƙara da cewa bayanin da ya bayar ya sa hukumar ta fahimci cewa ba a ma kammala dawo da kuɗin a lokacin da ake cewa an yi maimaitawar ba, kuma takardun lauya Enrico Monfrini na shekarar 2016 ma sun tabbatar da haka. Ya ce gwamnatin Buhari ta ki amincewa da kudin da Monfrini ya nema na gaba–gaba, ta kuma zaɓi lauyoyi ’yan Najeriya da suka ceto wa ƙasa makudan kuɗaɗe.

Malami ya bayyana cewa kudin da aka samu a bangarori daban-daban – ciki har da dala miliyan $322.5 daga Switzerland da aka yi amfani da su a shirin NSIP tare da kulawar Bankin Duniya, da kuma dala miliyan $321 daga Jersey da aka saka a manyan tituna kamar Lagos–Ibadan, Abuja–Kano da Zobe–Niger Bridge – ba su da alaƙa da juna, don haka zargin maimaitawa ba gaskiya bane. Ya kuma ce rahoton da ya danganta shi da wani tsohon hafsan soja kan ta’addanci ya riga ya wanke kansa a fili, sai dai kafofin yada labarai suka karkatar da batun.

A wani ɓangaren kuma, rahotannin EFCC sun tabbatar wa Kakaki24 cewa Malami na nan a tsare bayan ya kasa cika sharuddan belin da aka ba shi. Jami’in hukumar ya ce ana bincikensa kan manyan laifuka 18, ciki har da safarar kuɗi, cin zarafin ofis da kuma wasu tuhume-tuhume da ake ci gaba da gano su yayin bincike. Wani majiyar hukumar ya ce, “ba za mu sakeshi ba sai ya cika sharuddan belinsa.”

Malami ya nemi ’yan Najeriya su yi watsi da abin da ya kira “ƙage da farfaganda,” yana mai cewa abubuwan da ya taka rawa a kafa NFIU da dokokin AML/CFT na 2022 sun taimaka wajen fitar da Najeriya daga jerin ƙasashen FATF masu barazanar kuɗaɗen haram. Ya ce yana da tabbacin gaskiya za ta yi halarta duk da ƙoƙarin ɓata suna da siyasar ramawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet