Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Haramta Ƙirƙirar Kowace Irin Hukumar Hisbah a Jihar

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan wani umarnin zartarwa na musamman da ke haramta kafuwa da ayyukan duk wata ƙungiyar Hisbah ba tare da sahalewar gwamnati ba, musamman wata ƙungiya da ke kiran kanta da “Independent Hisbah Fisabilillahi”. An bayyana umarnin a hukumance ne a ranar 12 ga Disamba, 2025, ta bakin Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya.

Umarnin, mai taken “Kano State Government (Prohibition of the Independent Hisbah Fisabilillahi) Order 2025”, ya samo asali ne daga Sashe na 5(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), wanda ya ba gwamna ikon tabbatar da zaman lafiya, doka da oda a jiharsa.

Gwamnatin jihar ta bayyana damuwa mai tsanani kan yadda wasu mutane ke ɗaukar matasa, tsarawa da tara jama’a a ƙarƙashin wata ƙungiya ba tare da izinin doka ba, lamarin da ta ce yana haifar da tsarin tilasta doka na bogi da ka iya tayar da tarzoma tare da raunana aikin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano wadda ita ce kaɗai ke da hurumin doka.

A cewar Waiya, umarnin ya umurci ’yan sanda, DSS da NSCDC da su binciki masu shirya ƙungiyar tare da dakile duk wani aiki nasu. Ya kuma gargaɗi jama’a cewa duk wanda ya shiga, ya tallafa ko ya mara wa ƙungiyar baya, zai fuskanci hukunci bisa doka, inda aka buƙaci waɗanda aka riga aka ɗauka su janye nan take su kai rahoto ga hukumomin tsaro. Umarnin ya fara aiki nan take bayan gwamnan ya rattaba hannu a kansa a ranar 8 ga Disamba, 2025.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet