Featured
Tinubu Ya Sha Alwashin Turawa Ƙananan Hukumomi Ƙudinsu Kai Tsaye
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan da su yi biyayya ga hukuncin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu ba tare da tsoma bakin jihohi ba.
Shugaban ya yi gargaɗin cewa gwamnonin da suka ƙi aiwatar da hukuncin kotun za su tilasta masa ɗaukar matakin doka domin bai wa kansa ikon aikawa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun kwamitin rabon arzikin tarayya (FAAC).
Tinubu ya yi wannan gargaɗi ne a yayin taron majalisar zartarwar jam’iyyar APC karo na 15 da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya jaddada cewa hukuncin kotun ƙoli wajibi ne a mutunta shi. “Kotun ƙoli ta bayar da umarni gare ku. Idan kuka ƙi aiwatarwa, zan yi amfani da ikon shugaban ƙasa domin wuƙa da doya duk suna hannuna,” in ji Tinubu.
A ranar 11 ga watan Yulin 2024, kotun ƙoli ta yanke hukuncin da ya tabbatar da cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya, inda dukkan alƙalan kotun bakwai suka amince cewa dole ne a bai wa ƙananan hukumomi cikakken ikon tafiyar da kuɗaɗensu.
