Featured
Gwamnatin Tarayya Tace Da Amincewarta Amurka Ta Kawo Hari Sokoto
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da masaniya kuma sai da ya amince sannan sojojin Amurka suka kawo hare-haren sama kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar. Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a, sa’o’i kaɗan bayan Ma’aikatar Tsaron Amurka da Shugaba Donald Trump sun sanar da kai hare-haren.
Da yake magana a shirin Sunrise Daily na tashar Channels Television, Tuggar ya ce hare-haren hadin gwiwa ne tsakanin Najeriya da Amurka, kuma an tabbatar da cewa ba a kai su bisa wani dalili na addini ba. Ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya fayyace tun da farko cewa duk wata aiki da za a yi dole ne ta kasance ta hadin gwiwa kuma ba za ta nuna wariya ko nuna kai hari ga wani addini ba.
Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ƙasa ce mai addinai daban-daban, kuma tana aiki tare da ƙawayenta na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka, domin yaƙar ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Ya kuma musanta zargin cewa hare-haren sun karya ikon ƙasar, yana mai cewa gwamnatin tarayya ba za ta taba ɗaukar matakin da zai tauye ikon mallakar ƙasar Najeriya ba.
