Featured
Ƴan Sanda Sun Ƙwato Motar Sarkin Bauchi Da Aka Sace
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta sanar da kwato wata motar Toyota Hilux mallakin Majalisar Masarautar Bauchi da aka sace a cikin birnin Bauchi. Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce an samu nasarar kwato motar bayan samun rahoton satar ta.
Ya bayyana cewa direban motar ya sanar da jami’an sintiri cewa an sace motar ne a wata gidan mai, bayan ya tsaya na ɗan lokaci yayin da yake kan hanyarsa ta kai saƙon sarki zuwa ƙaramar hukumar Ganjuwa. Bayan samun rahoton, jami’an tsaro suka bi sawun wanda ake zargi.
A cewar ’yan sanda, an kama wanda ake zargi tare da kwato motar a yankin Bayan Gari, inda ya amsa laifinsa. Rundunar ta ce bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.
