Featured
An Kama Ƴan Najeriya 53 Kan Laifukan Damfara a Ghana
Hukumomin tsaron Ghana sun cafke mutane 53 da ake zargi da aikata manyan laifukan intanet a wani gagarumin samame da suka kai cibiyoyin damfara a birnin Accra da kewaye. Rahotanni sun nuna cewa dukkan waɗanda aka kama ’yan Najeriya ne.
Daga cikin adadin, mutum 44 an bayyana su a matsayin waɗanda aka yaudare su da alkawarin samun aiki, amma daga bisani aka tilasta musu aikata laifukan intanet, inda aka samu nasarar ceto su. Hukumomi sun ce samamen ya gudana tsawon kwanaki biyu bisa sahihan bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaron Intanet ta Ghana da sauran hukumomi.
A yayin aikin, an ƙwato kwamfutoci tafi-da-gidanka 62, wayoyin hannu 52 da bindigogi biyu, yayin da aka kama mutum tara da ake zargi su ne jagororin ƙungiyar. Ministan Sadarwa na Ghana, Sam George, ya ce an miƙa dukkan waɗanda aka cafke ga Hukumar Shige da Fice ta Ghana domin tsaro da ƙarin bincike.
