Featured
Tinubu Ya Ba da Umarnin Bincike Kan Kisan Uwa da ’Ya’yanta 6 a Kano
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi wa Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Chiranci ta Jihar Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin mugunta da ba za a amince da ita ba. Shugaban ya ce abin ya girgiza shi matuƙa, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar yankin da kuma gwamnatin Kano.
Tinubu ya yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya bisa cafke manyan waɗanda ake zargi cikin gaggawa, tare da umartar hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike. Ya jaddada cewa dole ne a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a lamarin, yana mai cewa irin waɗannan laifuka ba su da gurbi a cikin al’ummar Najeriya.
Shugaban Ƙasan ya kuma buƙaci jami’an tsaro su ƙara sa ido da ɗaukar matakan rigakafi kan aikata laifukan tashin hankali. Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su ba da haɗin kai ta hanyar isar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
