Featured
2027 : APC Za Ta Fuskanci Matsala Idan Ta Hana Ɗan Arewa Musulmi Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa – Hannatu Musawa
Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musawa, ta gargaɗi jam’iyyar APC da cewa za ta iya rage damar samun nasara a zaɓen 2027 idan ta cire Ɗan Arewa Musulmi daga tikitin sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu. Ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ta yi a shirin Mic On Show.
Musawa ta ce cire Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ko sauya shi da wanda ba Musulmin Arewa ba, zai jefa APC cikin matsala musamman a jihohin Arewa ta tsakiya. Ta ce siyasar Arewa na da zurfi sosai, kuma mutane na ɗaukar zaɓe a matsayin muhimmiyar hanya ta bayyana ra’ayinsu.
Ministar ta kuma ce jam’iyyun adawa ba su da tsari guda da zai iya kayar da Tinubu da Shettima a 2027, tana mai cewa adawar na cike da masu neman shugabanci iri ɗaya. Duk da haka, ta jaddada cewa APC na maraba da adawa mai ƙarfi domin bunƙasa dimokuraɗiyya, amma jam’iyyar na da cikakkiyar kwarin gwiwar ci gaba da mulki.
