Featured
Gwamna Abba Ne Jagoran APC a Kano – Ganduje
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya koma jam’iyyar APC a yau, yanzu shi ne jagoran jam’iyyar APC a jihar Kano.
Ganduje ya faɗi hakan ne yayin da yake jawabi a taron bikin komawar gwamnan APC da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Kano, inda ya ce jam’iyyar APC na maraba da shigar Abba Kabir Yusuf tare da mutanensa cikin jam’iyyar.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, bisa tsarin jam’iyyar APC, gwamna shi ne jagoran jam’iyya a kowace jiha, inda ya ce, “Don haka a nan ma, yanzu kai ne jagoran jam’iyyar APC a jiharmu ta Kano.”
