Featured
Manoma 3,500 Za Su Haƙura da Noman Shinkafa a Najeriya – Rahoto
Rahoton Kwamitin Manufofin Noma na Ƙasa (NAPM) ya bayyana cewa akalla manoman shinkafa 3,500 na shirin daina noma ko rage yawan noman shinkafa sakamakon asarar da suka yi wadda ta kai kimanin Naira biliyan 93 a lokacin daminar 2025. Rahoton ya samo asali ne daga binciken shirin yin manoman rani da aka yi wa manoma 33,507 a jihohi 13.
Kwamitin ya ce manoman shinkafa sun yi asarar Naira 20,220 a kowace hekta, inda yawan filayen shinkafa a Najeriya ya kai kusan hekta miliyan 4.6. Hakan ya sa manoma da dama ke sauya noma daga shinkafa da masara zuwa waken soya da sesame, saboda ribar da suke gani a kasuwannin duniya.
Rahoton ya danganta matsalar da manufofin shigo da shinkafa ba tare da haraji ba da gwamnatin Tarayya ta amince da su a watan Yulin 2024 domin rage hauhawar farashin abinci. Kwamitin ya shawarci gwamnati da ta rufe hanyoyin shigo da shinkafa, tare da kafa tsarin farashin kariya (Guaranteed Minimum Price) domin kare manoma da tabbatar da tsaron abinci a ƙasa.
