Featured
Gwamnatin Tarayya Na Tattaunawa da Amurka Don Cirewa Najeriya Takunkumin Biza
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana tattaunawa da Amurka ta hanyoyin diflomasiyya domin a cire Najeriya daga jerin ƙasashen da aka saka wa takunkumin bizar ƙaura. Matakin na Amurka, wanda aka sanar a ranar 14 ga Janairu, ya shafi ƙasashe 75 ciki har da Najeriya, kuma ya fara aiki daga 21 ga Janairu 2026.
Daraktan Yaɗa Labarai, Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare na Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce ba Najeriya kaɗai abin ya shafa ba, yana mai jaddada cewa ba za a iya tilasta wa wata ƙasa bayar da biza ba. Ya ce gwamnati na ci gaba da tattaunawa da Amurka don warware matsalar tare da fatan cimma matsaya mai amfani ga ɓangarorin biyu.
Ebienfa ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin kare muradun ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje, tare da ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da Amurka. Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa idan an warware dalilan da suka haifar da dakatar da bizar, za a cire Najeriya daga jerin ƙasashen da aka shafa.
