Featured
El-Rufai Zai Cigaba da Zama a Hannun ICPC Bayan Kotu Ta Ɗage Sauraron Buƙatar Belinsa Zuwa 14 Ga Afrilu
Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, zuwa ranar 14 ga Afrilu, 2026. Mai shari’a Rilwanu Aikawa ne ya bayyana hakan bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu a ranar Laraba.
An gurfanar da El-Rufai ne gaban kotu ta hannun hukumar ICPC kan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati. Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Kotun ta kuma umarci a ci gaba da tsare shi a hannun ICPC har zuwa ranar da aka ɗage shari’ar domin sauraron buƙatar belinsa. Rahotanni sun ce ya isa kotu da misalin ƙarfe 9 na safe tare da jami’an DSS, inda ya shiga cikin nutsuwa sanye da kaya riga da hula.
