Featured
Ministan Sufuri Ya Yi Murabus, Yayin da Ministan Lantarki Ya Musanta Batun Ajiye Aikinsa
Ministan sufuri, Sanata Saidu Alkali, ya ajiye aikinsa bayan wa’adin da gwamnatin tarayya ta bayar ga masu riƙe da mukaman siyasa da ke son tsayawa takara. Umarnin ya fito ne daga Shugaba Bola Tinubu, wanda ya buƙaci duk masu irin wannan buri su sauka kafin ranar 31 ga Maris, 2026.
Rahotanni sun ce Alkali ya ɗauki matakin ne domin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027, bayan ganawa da shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa. Haka kuma an tabbatar da cewa shugaban ya amince da murabus ɗin tare da yaba masa kan gudunmawar da ya bayar a ɓangaren sufuri.
A gefe guda kuma, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya hakura da burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo bayan ya kasa ajiye mukaminsa kafin wa’adin da aka gindaya. Mai taimaka masa ya bayyana cewa har yanzu yana kan aikinsa, yana mai karyata jita-jitar cewa ya yi murabus.
