Featured
Ƴan Majalisar Wakilai Huɗu Daga Kano Sun Fice Daga NNPP Zuwa ADC
Ƴan Majalisar Wakilai huɗu daga Jihar Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar ADC, a wani mataki da ke nuna sauyin siyasa gabanin zaɓen 2027. ‘Yan majalisar sun haɗa da Sani Wakili (Minjibir/Ungoggo), Muktar Zakari (Tarauni), Umar Datti (Kura/Madobi/Garun Malam) da Abdulhakeem Ado(Wudil/Gark).
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasiƙun ficewar nasu a zaman majalisa na ranar Laraba. Haka kuma wasu ‘yan majalisa daga jihohin Zamfara da Imo sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a lokaci guda.
‘Yan majalisar sun danganta ficewar tasu da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar tsofaffin jam’iyyunsu. Jam’iyyar ADC na ci gaba da karɓar sababbin ‘yan majalisa a ‘yan kwanakin nan, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
