Featured
Kotu Ta Bayar da Umarnin Tsare Waɗanda Ake Tuhuma da Yunƙurin Juyin Mulki a Hannun DSS
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare mutane shida da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulki a hannun hukumar DSS, bayan gurfanar da su kan tuhume-tuhume 13 da suka shafi ta’addanci. An fara shari’ar ne da misalin karfe 1:46 na rana a ranar Laraba.
A yayin zaman, Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, ya gabatar da tuhumar tare da neman a karanta wa wadanda ake zargin. Sai dai an dan dakatar da zaman bayan daya daga cikin wadanda ake tuhuma ya ce lauyansa ba ya nan, yayin da wani kuma ya bukaci a samar masa da mai fassara saboda Larabci da Hausa kawai yake fahimta.
Bayan ci gaba da zaman da misalin karfe 2:18 na rana, dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta laifukan tare da rokon a sake su. Kotu ta amince da bukatar masu kara na tsare su a hannun DSS tare da basu damar ganawa da lauyoyinsu, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 27 ga Afrilu, 2026 domin fara sauraron shari’ar cikin gaggawa.
