Featured
Akwai Yiwuwar Fuskantar Hare-haren Ta’addanci a Arewa-Maso-Gabas Yayin Bikin Sallah – Rundunar Soji
Hedikwatar haɗin gwiwar sojoji ta Operation Hadin Kai ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na shirin kai hare-hare a wasu wurare masu cunkoso a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya yayin bukukuwan Babbar Sallah.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar a Maiduguri, sojojin sun ce bayanan sirri sun nuna yiwuwar amfani da bama-bamai da kuma na’urorin fashewa a wuraren taruwar jama’a, musamman kasuwanni, tashoshin mota da filayen salla.
Rundunar ta shawarci jama’a da su gudanar da sallar Idi a kusa da unguwanninsu, su guji taruwar jama’a a fili mai yawa, tare da ƙara sa ido a wuraren jama’a da kuma kai rahoton duk wani abin zargi ga jami’an tsaro. Ta kuma tabbatar da cewa dakarunta suna cikin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan.
