Featured
NCDC Ta Gargaɗi ‘Yan Najeriya Kan Amfani Da Namijin Goro Da Ruwan Gishiri Don Maganin Ebola
Hukumar Nigeria Centre for Disease Control and Prevention ta gargaɗi ‘yan Najeriya da su guji amfani da goro mai ɗaci, ruwan gishiri, ganyaye da sauran magungunan gargajiya a matsayin maganin cutar Ebola. Hukumar ta ce babu wata hujjar kimiyya da ta tabbatar da cewa waɗannan abubuwa na magani ko kariya daga cutar.
NCDC ta bayyana hakan ne bayan yaɗuwar jita-jita a kafafen sada zumunta sakamakon bullar cutar Ebola a wasu ƙasashen Afirka kamar Congo da Uganda. Duk da cewa babu wanda aka tabbatar ya kamu da Ebola a Najeriya, hukumar ta ce ƙasar na cikin shirin ko-ta-kwana saboda zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe.
Hukumar ta buƙaci jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, tana mai cewa hakan na iya haddasa ruɗani da rage amincewar jama’a ga matakan kariyar lafiya. Darakta Janar na hukumar, Jide Idris, ya ce gano alamomin Ebola da wuri da kuma bin matakan kariya su ne mafi muhimmanci wajen dakile cutar.
