Connect with us

Featured

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci a Haramta Shigo da Yadika Najeriya

Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da dukkan nau’ikan kayan yadi daga ƙasashen waje domin farfaɗo da masana’antar yadi ta Najeriya. Haka kuma ta nemi Hukumar Kwastam ta ƙara sa ido a kan iyakoki domin dakile safarar kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan matsaya ta biyo bayan wani ƙuduri da Sanata Sunday Marshall Katung na Kaduna ta Kudu ya gabatar tare da goyon bayan wasu sanatoci tara. Ya bayyana cewa masana’antar yadi ta kasance ginshiƙin tattalin arziki musamman a yankin masana’antu na Kaduna da Kano, amma ta durƙushe sakamakon matsalolin ababen more rayuwa da rashin ingantattun manufofi.

Majalisar ta nuna damuwa cewa yanzu Najeriya na dogaro da kayayyakin yadi na ƙasashen waje wajen biyan sama da kashi 90 cikin 100 na buƙatun cikin gida. Don haka ta bukaci ma’aikatun noma da kasuwanci su ɗauki matakan gaggawa wajen farfaɗo da noman auduga da kuma masana’antun yadi a faɗin ƙasar, musamman a Kaduna da Kano.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet