Featured
Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa – Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a ci gaba da tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu. Obi ya yi wannan bayani ne yayin wata ganawa da ’yan Najeriya a birnin Washington DC na kasar Amurka.
Obi ya ce bai kamata a kama mutum saboda kalaman da ya yi a gidan rediyo ko kuma saboda ya soki wasu suka ba. Ya kara da cewa a matsayinsa na dan siyasa, ana yawan kiransa da sunaye daban-daban amma bai dauki hakan a matsayin laifi ba.
Ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zabe shi shugaban kasa, zai tattauna da duk masu rajin ballewa domin fahimtar matsalolinsu da nemo mafita. A cewarsa, tattaunawa ce kadai za ta taimaka wajen warware irin wadannan rikice-rikice. Kakaki24 ta ruwaito cewa Kanu na ci gaba da daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa na daurin rai da rai kan laifukan ta’addanci.
