Connect with us

Featured

Ya Kamata Ƴan Najeriya Su Haɗa-kai Domin Daƙile Matsalar Tsaro – Abdussalami Abubakar 

Tsohon Shugaban Najeriya na Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yakar matsalar rashin tsaro, yana mai cewa kawo karshen ta’addanci da sauran laifuffuka na bukatar hadin gwiwar al’umma, hukumomin tsaro da gwamnati a dukkan matakai.

A cikin sanarwar da ya fitar yayin bikin cika shekaru 84 da haihuwarsa, Abdulsalami ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar nan. Ya ce rasuwar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da sauran wadanda suka fada hannun rashin tsaro na nuna bukatar daukar matakan gaggawa.

Tsohon shugaban ya kuma yi gargadin cewa siyasantar da harkokin tsaro, yada labaran karya da bayanan bogi a kafafen sada zumunta na kara taimakawa masu aikata laifuffuka. Ya bukaci ‘yan Najeriya su ajiye bambance-bambancen addini, kabila da siyasa tare da mara wa jami’an tsaro baya domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa. – Kakaki24.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet