Featured
“Ban Ga Tsananin Yunwar Da Ƴan Najeriya Ke Magana a Kai Ba” — Bayo Onanuga
Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, inda ya ce shi da kansa bai ga irin yunwar da ake yawan magana a kanta a Najeriya ba.
Da yake magana a tashar Arise Television ranar Talata, Onanuga ya ce ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen gwamnati sun fara haifar da alfanu ga jama’a. Ya yi nuni da gyaran hanyoyi da kuma aikin titin gabar teku da ke rage wahalar sufuri ga masu zirga-zirga.
Ya kuma bayyana cewa shirye-shiryen rancen karatu da lamuni mai ƙarancin ruwa ga ma’aikata na taimaka wa ‘yan Najeriya, yana mai cewa duk da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, abubuwan da yake gani a mu’amalarsa da jama’a ba su nuna irin matsananciyar yunwar da ake yawan bayyanawa a bainar jama’a ba.
