Featured
Tambuwal Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Tabbatar Sun Kawo Ƙarshen Mulkin Tinubu a 2027
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su haɗa kai su kada kuri’a domin kawo ƙarshen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Ya zargi gwamnatin tarayya da gaza magance matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.
Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Sakkwato yayin karɓar tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Isa Salihu Bashir Kalanjeni, zuwa jam’iyyar ADC bayan ficewarsa daga APC. Ya yaba da matakin da Kalanjeni ya ɗauka, yana mai cewa ya kauce wa cin mutunci da zage-zage a harkokin siyasa.
Read Also : Majalisa Ta Buƙaci a Ƙaƙabawa Afirka ta Kudu Takunkumi Sakamakon Muzgunawa Ƴan Najeriya
Ya kuma ce gwamnati na cikin damuwa saboda ƙaruwar tasirin ADC, tare da yin kira ga magoya bayan jam’iyyar su ci gaba da gudanar da siyasa cikin lumana da mutunta juna. Ya kuma roƙi ‘yan Najeriya su yi amfani da hanyoyin dimokuraɗiyya wajen sauya gwamnati a zaɓen 2027.
