Featured
Obi Zai Rayu Har Zuwa Zaɓen 2027 Amma Tinubu Zai Sake Kayar Da Shi – Ministan Ayyuka
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya yi watsi da ikirarin Peter Obi cewa rayuwarsa na iya kasancewa cikin haɗari gabanin zaɓen 2027. Ya ce babu mai son ganin Obi ya mutu, yana mai cewa zai rayu ya tsaya takara amma kuma zai sake shan kaye a hannun Shugaba Bola Tinubu.
Umahi ya bayyana hakan ne yayin duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da ake yi a jihar Ebonyi. Ya ce fargabar Obi ta samo asali ne daga yadda yake ganin Kudu maso Gabas na ci gaba da goyon bayansa, amma ya ce yanayin siyasar yankin ya sauya sakamakon ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Read Also : INEC Ta Ƙara Wa’adin Mika Sunayen ‘Yan Takarar Zaɓen 2027
A nasa ɓangaren, Peter Obi ya zargi gwamnatin tarayya da hana shi wasu haƙƙoƙinsa tare da musguna masa saboda ra’ayinsa na siyasa. Sai dai fadar shugaban ƙasa ta musanta zarge-zargen, inda mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana ikirarin Obi a matsayin marasa tushe da nufin jan hankalin jama’a.
