Featured
Tinubu ya Gaji Ya Kamata Ya Yi Ritaya – Peter Obi
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya haƙura da neman sake tsayawa takara a zaɓen 2027, yana mai cewa shugaban ya gaji kuma ba shi da ƙarfin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce Tinubu na yanzu ba irin wanda ya jagoranci Jihar Legas a baya ba ne. Ya kuma zargi gwamnatin da gaza shawo kan talauci, yunwa da matsalolin tsaro.
Read Also : Akanta Janar Zai Gurfana Gaban Majalisa Kan Kasafin Kuɗin Hukumar Bogi
Ya ce rahotannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da talauci da ƙarancin abinci, yana mai cewa maimakon mayar da hankali kan waɗannan matsaloli, ‘yan siyasa sun fi karkata ga tattaunawar siyasa.
Obi ya jaddada cewa ba za a magance matsalar tsaro yadda ya kamata ba sai an rage talauci, an zuba jari a ilimi da samar da ayyukan yi. Ya kuma ce duk da yabon da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Tinubu kan tsaro, matakan da gwamnati ke ɗauka a yanzu ba su isa ba, yana mai cewa burinsa shi ne ganin Najeriya ta samu ci gaba da zaman lafiya.
