Connect with us

Featured

Ƴanbindiga sun kashe mutane a masallaci a Sokoto

Aƙalla mutum uku ne aka kashe a cikin wani masallaci, yayin da wasu da dama suka yi ɓatan dabo bayan ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Tsamaye da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun ce maharan sun isa ƙauyen da misalin ƙarfe 8:30 na daren Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i shida suna kai hare-hare, satar dabbobi da kayayyaki, tare da yin harbe-harbe. Sun kuma kewaye jami’an tsaro da ke yankin tare da hana su kai ɗauki.

Wani ganau ya ce mazauna garin sun gano gawarwakin mutum bakwai bayan maharan sun gudu. Ya ce uku daga cikin waɗanda aka kashe an hallaka su ne a cikin masallaci, yayin da biyar daga cikin waɗanda suka mutu ‘yan gudun hijira ne daga wasu ƙauyuka da hare-haren ’yan bindiga suka raba da muhallansu.

Maharatan sun kuma wawashe wasu shaguna, sun ƙona mota da wasu shaguna biyu. An tabbatar da sace aƙalla mutum uku bayan ’yan uwansu sun kira wayoyinsu, inda ’yan bindigar suka amsa tare da tabbatar da cewa suna hannunsu. Kakakin ’yan sandan Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar na sane da lamarin, amma tana jiran cikakken bayani.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet