Featured
Katsina : Ƴanbindiga sun yi yunƙurin sace alƙali ana tsaka da zaman kotu
Wani alƙalin kotun Musulunci, Mai Shari’a Muhammad Mukhtar, ya tsallake rijiya da baya bayan da ’yan bindiga suka kai hari a harabar kotun da yake shari’a a Gwarjo, Karamar Hukumar Matazu a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba 29 ga Yuli, lokacin da ’yan bindigar suka shiga kotun suna harbe-harbe tare da neman a nuna musu inda alƙalin yake. Sai dai alƙalin ya tsere ta wata ƙofa kafin su isa inda yake, inda wani mai babur ɗin haya ya taimaka wajen kai shi wani wuri mai aminci.
Shaidu sun ce harin ya jawo raunukan harbi ga mutane da dama, waɗanda aka garzaya da su asibiti a garin Matazu, kodayake ba a tantance ainihin adadinsu ba. ’Yan bindigar kuma sun yi barazanar kashe alƙalin idan ya sake zuwa yin zaman kotu a Gwarjo.
Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan kare rayukan jama’a da jami’an shari’a.
