Featured
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Kashe Naira Biliyan 37.6 Kan Tafiye-tafiye Cikin Shekaru Uku
Binciken bayanan kashe kuɗaɗen gwamnati ya nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe Naira biliyan 37.64 kan tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje, tare da wasu kuɗaɗen da suka shafi tafiye-tafiye daga watan Yunin 2023 zuwa Afrilun 2026. Bayanai daga GovSpend sun nuna cewa kuɗin sun haɗa da tafiye-tafiyen shugaban ƙasa da kuma kuɗin gudanarwa.
Bayanan sun kuma nuna cewa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje sau 51, inda ya shafe kusan kwanaki 261 a wajen Najeriya. Tafiye-tafiyen sun kai shi zuwa ƙasashe akalla 30, yayin da hutunsa na makonni uku a Turai ya ƙara yawan tafiye-tafiyensa zuwa sau 52.
Read Also : Atiku ya soki matakin Tinubu na tafiya hutu duk da irin matsalolin da Najeriya ke fuskanta
A cewar bayanan GovSpend, an kashe Naira biliyan 9.18 a rabin shekarar 2023, Naira biliyan 25.26 a shekarar 2024, da Naira biliyan 2.70 a shekarar 2025. Daga watan Janairu zuwa Afrilun 2026 kuma, Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe sama da Naira miliyan 477 kan tafiye-tafiye da sauran abubuwan da suka shafe su.
A gefe guda, bayanan sun nuna cewa an ware dalar Amurka 553,884 domin tafiye-tafiyen Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, tsakanin 2023 da 2024, wanda darajarsa ta kai Naira miliyan 700.7. Sai dai shugaban Transparency and Accountability Group, Ayo Ologun, ya buƙaci a binciki tushen kuɗaɗen da kuma sahihancin doka wajen kashe kuɗin.
