Featured
Talauci ne yasa matasa suke sayar da ƙodarsu – Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu matasa ’yan Najeriya na sayar da kodarsu domin samun kuɗin rayuwa. Ya danganta lamarin da tsadar rayuwa da yake cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu suka jawo.
Atiku ya ce ya samu labarai masu tayar da hankali game da yadda matasa ke komawa sayar da sassan jikinsu, musamman ƙoda, saboda matsananciyar buƙatar kuɗi. Ya yi zargin cewa wasu daga cikinsu na sayar da kodar a kan kuɗi kaɗan.
Read Also : Duk matar da mijinta ya hana ta zaɓar APC a 2027 ta kashe auren ta fito – Shugaban APC na Yobe
Ya ce tsadar abinci, sufuri, haya, kuɗin makaranta, magunguna da wutar lantarki na ƙara wa ’yan Najeriya wahalar rayuwa. Atiku ya bayyana cewa matasa ya kamata su kasance suna sayar da ƙwarewa, dabaru da sabbin tunane-tunane, ba sassan jikinsu ba, yana mai cewa dokokin da suka haramta cinikin gabobi kaɗai ba za su magance matsalar talauci da ke jefa mutane cikin wannan hali ba.
Atiku ya yi kira da a samar da sauye-sauyen tattalin arziki masu la’akari da jinƙan jama’a, ciki har da rage farashin abinci da sufuri, inganta kiwon lafiya da samar da ayyukan yi. Ya kuma ce rahotannin da ake samu kan safarar gabobin jiki sun ƙaru a baya-bayan nan, inda ’yan sanda suka gurfanar da wasu mutane da ake zargi da hannu a irin wannan aiki.
