Connect with us

Featured

Ina matukar godiya ga Tinubu sakamakon matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur – Dangote 

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma sassauta tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje. Ya bayyana matakan a matsayin muhimman sauye-sauye da gwamnati ta ɗauka.

Dangote ya bayyana hakan ne ranar Litinin a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya da ke Legas, yayin da yake ƙaddamar da sayar da hannayen jarin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals.

Read Also : Rikicin Boko Haram ya lalata makarantu sama da 5,000 a Borno – Zulum

Ya ce Rukunin Kamfanonin Dangote zai ci gaba da haɗa gwiwa da gwamnati wajen bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya. Dangote ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta samu sauyi, yana mai cewa bai yi tsammanin za ta kai matsayin da take a yanzu ba.

Sayar da hannayen jarin matatar Dangote da aka buɗe ranar Litinin ya ƙunshi sabbin hannun jari biliyan 4.1, kan N525 ga kowane hannun jari, yayin da mafi ƙarancin saye shi ne hannun jari 10 na N5,250. An tsara rufe sayar da hannayen jarin a ranar 13 ga Oktoba 2026.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet