Addini
Ɗariƙar Ƙadiriyya ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu a zaɓen 2027
Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga yunƙurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, lokacin da ya karɓi tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul’aziz Yari. Ya ce naɗa Yari a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC ya ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Ƙadiriyya da yaƙin neman zaɓen.
Read Also : OK Movement ta buƙaci NDC ta ba ta haƙuri kan kalaman shugaban jam’iyyar
Malamin ya ce shi da Yari sun kasance tare tsawon sama da shekaru 20, yana mai cewa Yari ya kasance yana goyon bayan gidan. Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ba wai kawai za ta goyi bayan sake zaɓen Tinubu ba ce, har ma tana ganin shugaban na da “kyakkyawar manufa” ga Najeriya.
Sheikh Qaribullah ya ce Ƙadiriyya za ta fara gudanar da addu’o’i ga Shugaba Tinubu, musamman kan zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kawo ƙarshen rashin tsaro. A nasa ɓangaren, Yari, wanda tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran mambobin tawagar suka raka shi, ya ce sun fara ganawa da malaman addini ne saboda irin girmamawar da suke musu.

Pingback: Dangote na duba yiwuwar zuba $10bn domin magance matsalar wutar lantarki a Najeriya - KAKAKI 24