Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da Hutu Domin Bikin Ranar ’Yancin Kai
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan ƙasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya ’yan Nijeriya da ke cikin gida da ƙasashen waje murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan ƙasar.
Read Also : Sarkin Kano ya yi Alla-wadai da lalata fastocin Gwamnan Kano, tare da umartar gaggauta gyara su
Ministan ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi amfani da bikin wajen nuna haɗin kai, kishin ƙasa, zaman lafiya da mutunta juna, tare da tunawa da muhimmancin haɗin kan ƙasa wajen samun ci gaba.
Tunji-Ojo ya ce duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, akwai fata na samun kyakkyawar makoma, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan ƙarfafa tsaro da inganta rayuwar jama’a.

Pingback: Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Wutar Lantarki Ta Sa’o’i 24 a Kano, Legas Da Wasu Birane - Ministan Lantarki - KAKAKI 24